Jam’iyyar APC ta jihar Filato ta kalubalanci Gwamna Caleb Mutfwang da ya fito fili ya bayyana sunayen mutanen da ke matsa masa lamba ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.
Gwamnan ya bayyana a wani taro a fadar gwamnati da ke Jos cewa wasu jiga-jigan APC sun roƙe shi da ya shiga jam’iyyarsu, amma ya ce sai idan Allah da kuma jama’ar jihar sun yarda zai iya yanke wannan shawarar.
Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar APC na riko a jihar, Shittu Bamaiyi, ya musanta ikirarin gwamnan, yana mai cewa wannan magana tana nuni ne da yadda gwamnatin Mutfwang ta gaza cika alkawuran da ta dauka ga al’umma,inda ya ce idan gaskiyane ya fito ya faɗi sunayen waɗanda ke matsa masa lamba, ya kuma bayyana su.



