Shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da Majalisar Dokoki domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe, adalci da gaskiya a Nijeriya.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da hukumar INEC ta fitar a ranar Litinin, inda Amupitan ya bayyana cewa hukumar INEC za ta yi aiki kafada da kafada da ‘yan majalisa wajen sake duba dokar zabe domin tabbatar da cewa sabbin gyare-gyare za su ɗauki darussa daga zabubbukan da aka yi a baya, tare da ƙara gina amincewar al’ummar Nijeriya ga hukumar zabe.
Ya ce manufar wannan gyara ita ce rage yawan ƙorafe-ƙorafen zabe ta hanyar tabbatar da gaskiya da adalci a kowane mataki na zabe ga kowane bangare.
Ya kara da cewa, doka ce ginshiƙin tabbatar da dimokuraɗiyya, don haka dole ne ayi abinda zai hana rikice-rikicen sakamakon zabe.



