DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar agajin gaggawa NEMA ta karɓi ƴan Nijeriya 153 da suka makale a Chadi

-

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA, ta bayyana cewa ta karɓi ’yan Nijeriya 153 da suka dawo daga ƙasar Chadi, ƙarƙashin shirin Ƙungiyar Kula da Ƴan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya.

Kamar yadda sanarwar ofishin NEMA na Legas ta nuna a shafin X ranar Talata, matafiyan sun iso filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Lahadi, 27 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 12:15 na rana, ta jirgin ASKY Airlines mai lamba CAS-AC.

Google search engine

Sanarwar ta ce cikin matafiyan da suka dawo akwai manya 105 (maza 63 da mata 42), yara 45 (maza 25 da mata 20), da jarirai 3, dukkaninsu mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaban Amurka Donald Trumph ya haramtawa Farfesa Wole Soyinka zuwa kasar

Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaba Donald Trump ta soke takardar izinin shiga ƙasar ga Farfesa Wole Soyinka, sanannen marubuci a duniya. Farfesa Soyinka ya bayyana hakan...

Mun raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624 – Asusun NELFUND

Asusun ba da bashin karatu ga ɗaliban manyan makarantu ya bayyana cewa ya raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624, tun bayan...

Mafi Shahara