DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tinubu ya cire masu manyan laifuka daga jerin wadanda za su amfana da afuwar shugaban kasa

-

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan takardun afuwa da sassauta hukunci ga wasu mutane da aka taɓa yanke wa hukunci, domin aiwatar da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na yin afuwa.

Kamar yadda sanarwar fadar shugaban ƙasa ta bayyana a ranar Talata, 29 ga Oktoba, 2025, matakin ya biyo bayan tattaunawa da Majalisar Koli ta Ƙasa da kuma ra’ayoyin jama’a game da batun.

Google search engine

Shugaban ƙasa ya kuma bada umarnin sake nazarin jerin sunayen wadanda aka fara tsara yi musu afuwa domin tabbatar da adalci da tsaro.

Sanarwar ta ce an cire sunayen wadanda suka aikata manyan laifuka kamar sace mutane, fataucin miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, damfara, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, daga jerin.

Wasu kuma da aka riga aka yi musu afuwa a baya, an rage musu hukunci ne kawai ba a sake su gaba ɗaya ba.

A cewar gwamnatin tarayya, wannan mataki ya zama dole saboda muhimmancin tsaron ƙasa, jin tausayin waɗanda aka yi wa laifi, da kuma girmama ƙoƙarin hukumomin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Tinubu ta fitar da Naira biliyan 2.3 don biyan bashin albashi da karin girma na malaman jami’o’i

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta saki kudin da ya kai Naira biliyan 2.3 domin biyan bashin albashi da karin girma na malamai a jami’o’in...

Majalisar wakilan Nijeriya ta amince wa Tinubu ya ciyo bashin dala biliyan 2.35

Majalisar wakilai ta Nijeriya ta amince da bukatar shugaban Tinubu na neman bashin dala biliyan 2.347 daga ƙasashen waje domin cike gibin kasafin kuɗin 2025...

Mafi Shahara