Gwamnatin Nijeriya ta musanta maganganun shugaban Amurka, Donald Trump, da ke cewa ana yawan kisan Kiristoci a Nijeriya tare da kiranta “kasa mai matsalar tauye ‘yancin addini.”
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a safiyar Asabar, gwamnatin ta ce wadannan zarge-zargen ba su da tushe kuma ba su bayyana ainihin halin da ake ciki a kasa ba.
Sanarwar ta kara da cewa, karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya na ci gaba da yaki da ta’addanci tare da karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai, da kuma kare rayuka da hakkin ‘yan kasa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Hakazalika, sanarwa ta ce gwamnatin Nijeriya za ta cigaba da tattaunawa da gwamnatin Amurka domin kara fahimtar juna kan kokarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.



