DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna jihar Plateau ya musanta komawa APC

-

Gwamna Caleb Mutfwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya nesanta kansa daga jita-jitar da ake yadawa ta cewa ya koma jam’iyyar APC.

Wannan dai na a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Gwamnan jihar, Gyang Bere.

Google search engine

Sanarwar ta bayyana cewa wannan wani yunkuri ne da wasu bata gari ke yi domin raba kan al’ummar jihar.

A cewar sanarwar, Gwamna Mutfwang na hada kai da gwamnatin tarayya domin ci gaban jihar Filato.

A watannin baya dai gamayyar kungiyoyin jam’iyyar APC a Arewa ta tsakiyar Nijeriya karkashin jagorancin Hon. Saleh Zazzaga ta yi ta kiran gwamnan kan ya dawo jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara