Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya kafa kwamiti na musamman domin sasanta dukkan bangarorin da ke cikin sabani kafin babban taron zaben shugabanni na kasa da za a gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.
Wannan mataki ya fito ne daga wani taron gaggawa da kwamitin ya gudanar a ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamba, 2025, an Abuja.
Kwamitin sulhun mai mutum shida zai kasance karkashin jagorancin Ambasada Hassan Adamu daga Arewa maso Gabas, tare da Cif Mike Oghiadomhe daga Kudu maso Kudu a matsayin sakatare. Ana sa ran kwamitin zai mika rahotonsa kafin 11 ga watan Nuwamba, 2025.
Kwamitin amintattun ya yaba da kokarin kwamitin riko karkashin jagorancin Damagum da sauran kungiyoyin jam’iyyar wajen kwantar da rikice-rikicen cikin gida, tare da gode wa kotun Jihar Oyo bisa hukuncin da ta yanke na amincewa da jam’iyyar ta gudanar da nata al’amura ba tare da katsalandan ba.



