DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan Nijeriya sama da miliyan 1 sun rasa Muhallansu – Hukumar kididdiga ta NBS

-

Hukumar Kididdiga ta Nijeriya NBS ta ce yanzu haka kimanin mutane miliyan 1 da dubu 134 da 828 daga gidaje dubu 251da 82 ne ke gudun hijira a kasar. 

Google search engine

NBS ta bayyana hakan ne a wani rahoto da ta fitar a baya-bayan nan, inda ta bayyana jihar Borno a matsayin wadda ta fi kowacce yawan mutanen da ke gudun hijira da yawansu ya kai dubu 877 da 299, kwatankwacin kashi 77 da digo 3 na daukacin al’ummar jihar da aka kidaya. 

Rahoton ya kuma bayyana cewa an gudanar da binciken ne a shekarar 2023 a jihohin Adamawa da Yobe da Borno da Sokoto da Katsina da Benue da Nasarawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wike ya musanta jita-jitar tsayawarsa takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027, ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu har zuwa 2031

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya karyata rahotannin da ke cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na matsa masa lamba domin ya tsaya takarar shugaban ƙasa a...

Sau 22 ana yunkurin lalata mana matatar mai – Matatar man fetur ta Dangote

Kamfanin matatar mai ta Dangote ya bayyana cewa tun bayan da matatar man da ke fitar da ganga 650,000 a rana ta fara aiki, aƙalla...

Mafi Shahara