DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Matukar dimokradiyya ta gaza a Nijeriya sai ya shafi fadin Yammacin Afrika – ECOWAS

-

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a duk faɗin Yammacin Afrika, kamar yadda shugaban hukumar, Omar Touray, ya bayyana a wajen kaddamar da shirin “Regional Partnership for Democracy” a Abuja.

Wakilinsa, Abdel-Fatau Musah, ya ce dimokuradiyya na cikin tsananin barazana a yankin, yana yaba wa Nijeriya, Ghana, Senegal da Cabo Verde bisa tsayuwa kan tsarin jam’iyyu da dama, tare da nanata cewa matsalar Nijeriya na iya shafar makomar yankin baki ɗaya.

Google search engine

Musah ya yi kira ga ƙasashen Yammacin Afrika su sake nazarin wa’adin shekara huɗu na shugabanci saboda rashin wadatar da yake yi wajen aiwatar da manyan shirye-shirye da kuma gina dimokuradiyya mai ɗorewa.

Haka kuma, ya bayyana kalubalen da ke barazana ga tsarin mulki a yankin, ciki har da juyin mulki, amfani da kotu wajen karkatar da doka, da kuma hana jam’iyyun adawa damar shiga siyasa, yana mai cewa wa’adin shekara huɗu ba ya wadatarwa ga ƙasashe irin su Nijeriya da Ghana wajen magance matsalolin ci-gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawa ta bukaci a dauki matasa aikin tsaro domin magance matsalar tsaro

Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla...

PDP tsagin Wike ta kori Bala Muhd da Dauda Lawan, gwamnonin Bauchi da Zamfara

Jam’iyyar PDP ta kara shiga wani sabon rikici a ranar Talata bayan bangaren kwamitin zartaswa da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar...

Mafi Shahara