Gwamnatin Jihar Katsina ta bada umarnin rufe dukkan makarantu sakamakon tsananin barazanar tsaro da ake fuskanta a arewacin kasar, musamman bayan sace dalibai a Jahohin Neja da Kebbi. Kwamishinan Ilmi na Jihar ya tabbatar da hakan, inda ya ce matakin ya zama dole domin kare rayuwar dalibai da malamai.
Wannan batu ya yi karfi musamman idan aka yi la’akari da wani sabon rahoto da ya nuna cewa sama da yara 300,000 a Katsina ba sa zuwa makaranta saboda tsaro mai rauni.
DCL Hausa ta ruwaito cewa gwamnati na duba yiwuwar sake fasalin tsaron makarantun jihar, yayin da ake cigaba da kai hare-hare a makarantu daban-daban a arewacin kasar. Masu sharhi dai na ganin cewa rufe makarantu ka iya kare rayuka, amma hadarin da yake haifarwa ga makomar ilimi ya fi tsanani idan ba a dauki matakan gaggawa ba.



