Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya ce gwamnati ba ta gurfanar da waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin ta’addanci ba saakamakon binciken yana da sarkakiya, ba kuma abin da za a hanzarta shi ba ne duk da matsin lambar jama’a.
Jaridar Punch ta ruwaito Idris ya ce, ba wai da an samu jerin sunaye ne kawai za a garzaya kotu ba, yana mai cewa dole a tattara bayanai sosai kafin daukar mataki. Wannan na zuwa ne yayin da ake ƙara zargin gwamnati da rashin gaskiya kan yawaitar hare-haren tsaro.
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu na aiki tukuru wajen murƙushe ta’addanci, inda ya bayyana cewa tun daga Mayu 2023 sama da ’yan ta’adda 13,500 aka hallaka, fiye da 17,000 kuma aka kama, wasu ma na fuskantar shari’a yanzu.



