DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babu abin da ke tada mun hankali irin matsalolin tsaron da ya addabi Nijeriya – Shugaba Tinubu

-

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce matsalar tsaro ita ce babbar damuwar Nijeriya, musamman Arewacin ƙasar, yana mai cewa dole a hanzarta dawo da zaman lafiya da haɗin kai.

Da yake magana a Kaduna ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, a bikin cika shekara 25 na kungiyar tuntuba ta Arewacin Nijeriya, ACF, ya ce gwamnati na aiki da hanzari don murkushe ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke lalata tattalin arziƙi da ilimi.

Google search engine

A cewarsa, babu abin da ke tayar masa da hankali irin matsalolin tsaro musamman a Arewacin kasar inda ya ce ba za a ci-gaba ba matukar wani bangare na kasar na cikin matsala kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gaji matsaloli masu tsanani amma tana tunkararsu, yana fatan Arewacin Nijeriya za ta farfaɗo tare da manyan ayyuka kamar titin Abuja–Kaduna–Kano da kuma rijiyar mai ta Kolmani da ake sa ran za su farfado da tattalin arziƙi.

Hakazalika, Tinubu ya yaba wa ACF bisa zama murya ɗaya ta Arewa, yana gargadin cewa yankin ba zai ci-gaba ba idan shugabanni suka kasa kare marasa ƙarfi, musamman yayin da jama’a ke fama da tsoro da yunwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun yi nadamar yekuwar a ba Yilwatda shugabancin APC – Kungiyar magoya bayan jam’iyyar na Arewa ta tsakiya

Kungiyar magoya bayan jam'iyyar APC a Yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta bayyana nadamarta bayan ta dage kai da fata sai an naɗa dan yankin...

Kungiyar tarayyar Turai za ta tallafa ma gwamnatin Nijeriya da Yuro miliyan 45 don inganta fasahar zamani

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) tare da abokan huldarta sun kaddamar da sabon mataki na hanzarta sauyin fasahar dijital a Nijeriya, yayin taron kwamitin kula da...

Mafi Shahara