Kungiyar Tarayyar Turai (EU) tare da abokan huldarta sun kaddamar da sabon mataki na hanzarta sauyin fasahar dijital a Nijeriya, yayin taron kwamitin kula da cibiyar sauyin fasaha da aka gudanar a Kano, kana aka bude Women Venture Studio Innovation Hub.
A cikin shirin, EU za ta bayar da karin tallafin Yuro miliyan 45 ga shirin 3MTT na gwamnatin tarayya, wanda ke da nufin horas da ‘yan Nijeriya miliyan uku a fannoni na zamani kamar AI, tsaron yanar gizo da kirkirar manhajojin komfuta.
Shugabar sashen Green and Digital Economy na EU, Inga Stefanowicz, ta ce manufar ita ce tabbatar da cewa cigaban fasaha ya kasance na kasa baki daya, inda ta jaddada cewa nan da 2025 za a fadada horo da bunkasa fasahar zamani a dukan sassan Nijeriya.



