Jam’iyyar PDP ta na shawartar Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nemi taimako ko ya yi murabus, sakamakon yawaitar hare haren ‘yan bindiga da sace sacen ɗalibai da ya addabi jihohin Arewa a kwanakin nan.
A wani taron manema labarai da jam’iyyar ta yi a Abuja, mai magana da yawunta na ƙasa Ini Ememobong ya ce sace ɗalibai a jihar Kebbi da Niger da kuma masu ibada a Kwara na nuna gazawar Gwamnatin Tinubu wajen magance matsalar tsaro.
A cewar sa gwamnati ta gaza aikinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, yana mai jaddada cewa idan gwamnati ta kasa wannan aiki to ga dole ta nemi taimako daga cikin gida ko wajen ƙasa.
PDP ta ce matakin rufe wasu makarantun da wasu jihohi ke yi babu inda zai kai, domin hakan kamar mika wuya ne ga ‘yan ta’adda.



