DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe dukkanin makarantun da ke fadin jihar

-

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkan makarantu firamare, sakandare da manyan makarantu ciki har da na masu zaman kansu sakamakon matsalar tsaro.

Rufe makarantun ya biyo bayan munanan hare-hare da aka kai kwanakin nan ciki har da sace dalibai a jihohin Neja da Kebbi.

Google search engine

Haka kuma ‘yan bindiga sun halaka ‘yan sanda biyar a kauyen Sabon Sara a ƙaramar hukumar Darazo ta jihar kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Bauchin ta tabbatar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Ilimi ta jihar Bauchi Jalaludeen Usman ya fitar, gwamnati ta ce rufe makarantun ya biyo bayan tattaunawa da hukumomin tsaro tare da la’akari da tsaron dalibai da malamai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sace dalibai na barazana ga makomarsu a Arewacin Nijeriya – Amnesty International

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International a Nigeria ta yi gargadin cewa yawaitar sace dalibai a makarantun arewa na iya karya ilimi, tare...

Makarantun Sakandire na je-ka-ka dawo za su ci gaba da karatu – Gwamnatin Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta bai wa makarantun firamare da sakandare na je-ka-ka-dawo damar ci gaba da karatu A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta...

Mafi Shahara