DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Makarantun Sakandire na je-ka-ka dawo za su ci gaba da karatu – Gwamnatin Katsina

-

Gwamnatin jihar Katsina ta bai wa makarantun firamare da sakandare na je-ka-ka-dawo damar ci gaba da karatu

A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar, ta ce anyi haka ne domin ba da damar zana jarabawar zangon karatu na farko.

Google search engine

Sanarwar ta ce duk da haka dukkannin makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai bayan wani sabon umarni bisa matakan da Gwamnatin jihar Katsina ta dauka don ƙara tsaurara tsaro da kare rayukan ɗalibai da malamai a fadin jihar.

Ma’aikatar ta umurci shugabannin makarantun je-ka-ka dawo da sauran masu ruwa da tsaki su kiyaye tsari da bin dokoki tare da kira ga iyaye su ba ’ya’yansu cikakken goyon baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sace dalibai na barazana ga makomarsu a Arewacin Nijeriya – Amnesty International

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International a Nigeria ta yi gargadin cewa yawaitar sace dalibai a makarantun arewa na iya karya ilimi, tare...

Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe dukkanin makarantun da ke fadin jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkan makarantu firamare, sakandare da manyan makarantu ciki har da na masu zaman kansu sakamakon matsalar tsaro. Rufe makarantun...

Mafi Shahara