Home Sabon Labari Sojojin Nijar da suka mutu a harin Chinegodar sun karu zuwa 89

Sojojin Nijar da suka mutu a harin Chinegodar sun karu zuwa 89

86
0

Mai magana da yawun gwamnatin Abdurahaman Zakaria ya bayyana cewa sojojin kasar 89 ne suka rasa ransu a yayin harin maimakon 25 da gwamnatin ta bayyana a baya tare da kashe ‘yan ta’addar 77.

A daren ranar litinin din nan ne kakakin gwamnatin jamhuriyar Nijar ya bayyana a kafar talabajin din kasar dan sake bada karin haske akan harin da ya afku a shingen jami’an tsaron kasar na Chinegodar da ke cikin jihar Tillabery a ranar alhamis din nan da ta gabata

Wannan sanarwa ta ranar Lahadi da daddare dai ta zo ne bayan labaran da suka mamaye kafafen yada labaran kasar Nijar da na ketare, inda ake rinka musanta adadin sojojin da suka rasa ransu fiye da yadda gwamnati ta bayyana a sanarwarta ta farko.

Shugaban kasar Nijar Mouhamadou Isoufou

Tun a ranar  Asabar dai a wajen jana’izar sojojin a birnin Yamai al’umma ta lura cewa adadin sojojin da suka rasa ransu a harin yafi wanda gwamnatin ta bayyana.

A yanzu gwamnatin ta bayyana kwanaki uku (3) na zaman makoki a duk fadin kasar.

Wannan hari dai na zama mafi muni da kasar ta fuskanta daga ‘yan ta’addar masu ikirarin jahadi da ake zargin na fitowa daga kasar Mali wanda yazo kasa da wata guda da kawo wani kazamin harin da ya yi sanadiyar rasa ran sojojin 71 a Inates duk a cikin jihar Tillaberi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply