DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 512

Abba Gida-gida ya bayyana kadarorinsa kafin fara aiki


Gabanin a yi bikin rantsar da shi a ranar Litinin, zababben gwamnan jihar Kano, Injiniya. Abba Kabir Yusuf ya bayyana ilahirin kaddarorin da ya mallaka da kuma bashin da ake bin shi a cikin wani kumshin takardu da ya mika a ranar Juma’a ga ofishin da’ar ma’aikata na jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa zababben Gwamnan wanda ya samu tarba daga Daraktar a hukumar ta CCB ta jihar Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ya ce kwazonsa na bayyana kadarorin da ya yi nuni ne na gaskiya da rikon amana da zai zama ginshikin a gwamnati mai zuwa a jihar Kano.

Da yiwuwar farkon gwamnatina ya yi tsauri – Tinubu

Zababben shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce duba da irin matsalolin da ke ci wa Nijeriya tuwo a kwarya a halin yanzu, da yiwuwar farkon mulkinsa ya dan yi tsauri. Sai dai Bola Tinubu ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa cikin kankanin lokaci za a shawo kan wadannan matsaloli su fara darawa.
Bola Tinubu na magana ne a Abuja bayan kammala sallar Juma’a da yin adu’o’i a wani bangare na bukukuwa kafin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Zababben shugaban kasar da ya samu wakilcin mataimakinsa Kasshim Shettima ya ce akwai tarin matsaloli sannan ga kankanin lokaci da gare su na kokarin shawo kan wadannan matsaloli.

Za mu dawo mulkin Kano ba dadewa – Ganduje

Gwamnan Kano mai barin gado Abdullahi Ganduje, PhD
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce za su bar Gwamnati a jihar na dan wani lokaci amma za su dawo su amshi mulki ba da jimawa ba.
Ganduje ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi lokacin bikin bude aikin sabo titin kwanar Dala a karamar hukumar ta Dala.
“Tabbaas tarihi zai sake maimaita kansa na Dawo-dawo dama wancan Dawo-dawon din ma mu muka sa aka yi ta, Kuma mu muka san dawo-dawo, don haka a wannna lokacin ma kada mu manta da wakar nan ta Dawo-dawo” Inji Gwamna Ganduje.

Daraktan sufuri a Nijar ya halaka kanshi


Daraktan sufuri a jihar Tillaberi ta Jamhuriyar Nijar Adamou Halidou ya halaka kansa, inda ya mutu ta hanyar rataye kansa a saman bishiya.

Adamou Halidou wanda dan asalin garin Dogon Doutchi ne na jihar Dosso ta kasar ya rataye kansa a wata bishiya a ranar Larabar nan.
Daraktan sufuri a Nijar dai, kwantankwacin kwamishina ne a mukaman da ake rabawa a jihohin Nijeriya.