Sunday, April 5, 2026
Home Blog

Gwamnatin Kano ta yi alwashin ci gaba da hadin guiwa da gwamnatin Tinubu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin kawo ayyukan ci gaba da tallafin gwamnatin tarayya zuwa jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar, bayan dawowar gwamnan Kano daga Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen samar da romon dimokuraɗiyya ga al’umma, musamman a muhimman fannoni kamar ci gaban tattalin arziki, abubuwan more rayuwa da walwalar jama’a.

Wani matashi ya yi ajalin mahaifinsa a jihar Jigawa

Wani matashi mai shekaru 27, Kabiru Nuhu, ya shiga hannun ‘yan sanda a Jihar Jigawa bisa zargin hallaka mahaifinsa mai shekaru 60 har lahira a ƙaramar hukumar Kazaure.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Adam, ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya zuba mai kamar fetur a jikin mahaifin nasa kafin ya banka masa wuta a unguwar Magama da ke garin Kazaure da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar ranar 1 ga Afrilu, 2026.

Ya ce an garzaya da wanda aka yi ajalin asibiti, amma ya rasu yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarsa, amma an kama wanda ake zargin dauke da raunukan konewa a jikinsa.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, tare da shirin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Haruna Yahaya, ya yi Allah-wadai da lamarin tare da kira ga jama’a su rika warware rikice-rikice cikin lumana.

Nijeriya za ta magance matsalolin tsaron da ke addabarta – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa za shawo kan matsalar ta’addanci da rashin tsaro, yana mai jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Shugaban ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da filin jirgin sama na Gateway International Cargo Airport a jihar Ogun.

Tinubu ya bayyana cewa ƙarfafa tsaro na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa, tare da bunƙasa tattalin arziki da ayyukan more rayuwa.

Ya ce muhimmantar da harkar tsaro da haɗin gwiwar ƙasa baki ɗaya za su taimaka wajen murkushe barazanar hare-haren ‘yan ta’adda a faɗin kasar.

Ministar Kwadago a gwamnatin Tinubu ta yi murabus daga mukaminta

Nkeiruka Onyejeocha ta yi murabus daga muƙaminta na Karamar Ministar Kwadago da Ayyuka domin shirin takarar zaɓen 2027.

Ta zama ta uku cikin ministocin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da suka ajiye aiki, bayan umarnin shugaban Nijeriya ga masu niyyar tsayawa takara su sauka kafin ƙarshen Maris.

Ta sanar da murabus ɗin nata ne ta cikin wata wasiƙa da ta wallafa a shafukan sada zumunta, amma ba ta bayyana kujerar da take shirin nema ba.

Ministar ta gode wa shugaban Nijeriya da ma’aikatan ma’aikatar bisa haɗin kai, tana mai cewa za ta ci gaba da hidimtawa ƙasa a wani sabon mataki.

Tsohon gwamnan Benue, Ortom, ya musanta jita-jitar tsayawa takarar Sanata a 2027

Tsohon gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin tsayawa takarar Sanata a zaɓen shekarar 2027.

Jaridar Punch ta rawaito cewa rahotanni sun bazu a kafafen sada zumunta a ranar Juma’a, inda aka riƙa cewa tsohon gwamnan na da niyyar komawa siyasa.

Ortom, wanda ya mulki jihar daga 2015 zuwa 2023, ya taba tsayawa takarar kujerar sanata a 2023 amma ya sha kaye a hannun tsohon mai taimaka masa Sanata Titus Zam.

Muna kira ga ‘yan Nijeriya kar su sake zabar Tinubu saboda gazawa wajen samar da wutar lantarki – Peter Obi 

Tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen 2023 Peter Obi, ya bukaci ‘yan kasar kada su sake zaɓen Shugaba Tinubu, yana mai danganta hakan da gazawa wajen inganta wutar lantarki a ƙasar.

Obi ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya tuna cewa Tinubu ya yi alkawarin idan bai samar da wutar lantarki mai dorewa cikin shekaru huɗu ba, kada a sake zaɓensa.

Ya ce a halin yanzu alkawarin bai cika ba saboda samun wutar lantarki ya ragu daga sama da megawatt 4,000 a shekarar 2023 zuwa ƙasa da haka yanzu, yayin da kuma farashin lantarki ke karuwa sossai.

NLC ta bukaci ma’aikatan jihohin da ba su aiwatar da mafi karancin albashi su gudanar da zanga-zanga

Kungiyar ƙwadago a Nijeriya NLC, ta umarci ma’aikata a jihohin da ba su aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ba, su gudanar da bikin May Day na 2026 a kan tituna maimakon wuraren taro na gwamnati.

A cikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja ya fitar, ya zargi wasu gwamnatocin jihohi da karya dokar sabon valbashi ta 2024, musamman wajen rashin biyan cikakken albashi, rashin gyara albashin manyan ma’aikata da kuma kin shigar da ma’aikatan kananan hukumomi, malamai da ma’aikatan lafiya cikin tsarin.

Kungiyar ta bayyana cewa irin wannan mataki na jihohi cin zarafi ne ga hakkin ma’aikata, tare da cewa dokar albashi da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu wacce ta sauya albashi daga naira 30,000 zuwa 70,000 ba ta samu cikakken aiwatarwa ba a wurare da dama.

NLC ta bukaci ma’aikata su taru daga karfe 7 na safe a ranar 1 ga watan Mayu su fito zanga-zanga cikin lumana a manyan biranen jihohi, inda za su kai korafe-korafensu ga gwamnati, tana mai cewa rashin yin hakan zai zama kamar cin amanar gwagwarmayar ma’aikata.

Gwamna Dauda Lawal ya lashe kyautar gwarzon gwamnan shekara a birnin London

LGwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya lashe kyautar gwarzon gwamnan shekara ta mujallar ‘Triangle Media International’ a birnin London.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa ana bayar da kyautar ne ga jagorori wadanda tasirin shugabancinsu ya bayyana a zahiri.

Ba za a fara tura wa mahajjatan Nijeriya kudin guzuri ta asusun banki a wannan shekarar ba – NAHCON

Babban Bankin Nijeriya CBN ya amince da amfani da tsabar kuɗi ga alhazan Nijeriya a Hajjin 2026 a matsayin kudin guzuri maimakon tsarin kati da ake shirin fara amfani da shi.

Matakin ya biyo bayan roƙon da Hukumar Alhazai ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Ismail Abba Yusuf ta yi domin rage damuwar maniyyata kan sauyin tsarin.

CBN ta ce wannan sassauci na wucin gadi ne, inda ta jaddada cewa daga Hajjin 2027 za a kma tsarin biyan kuɗi ta asusun banki gaba ɗaya.

Masu ruwa da tsaki sun ce matakin zai taimaka wajen kauce wa matsaloli, yayin da ake shirin wayar da kan alhazai kan sabon tsarin kafin a fara aiwatar da shi.

‘Yan sandan Abuja sun ceto wata mata mai tabin hankali da jaririyarta

Rundunar ‘yan sandan Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa a ranar 3 ga Afrilu, 2026 da misalin karfe 12:30 na dare, jami’an Rapid Response Squad da ke sintiri a yankin Kwali sun gano wata mata mai tabin hankali da mace a bakin hanya a kauyen Kwaita.

A sanarwar da SP Josephine Adeh ta aike wa DCL Hausa, ta ce jami’ansu sun kai matar da jairiryarta Asibitin Kwali inda aka ba su kulawar lafiya kafin a sallame su cikin koshin lafiya, sannan aka mika su ga jami’in jin kai na karamar hukumar Kwali, Malam Sadiq Kwali.