DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
Home Blog Page 519

Mutanen Kaduna na fargabar rusau daga Uba Sani

Ayyuka na farko-farko da Uba Sani ya fara yi a matsayin sabon gwamnan jihar Kaduna a ranar 29 ga watan Mayu, sa’o’I kadan bayan da aka rantsar da shi, su ne sanar da sauya sunan sanannen titin nan na Rabbah Road zuwa Malam Nasir El-Rufa’i road, abin da ya razana wasu da suka yi fatan sabon gwamnan ya kauce wa manufofin tsohon gwamnan da aka yi wa lakabi da “mai rusau”. An zargi El-Rufai dai da bijirowa mutanen jihar da manufofi masu tsauri a zamanin mulkinsa. To sai dai kuma wasu na ganin hakan ba wani abu ba ne illa godiya da girmamawa ga tsohon gwamnan, ganin irin tsayin dakar da Elrfufai ya yi wajen ganin Uba Sanin ya zama gwamna.

Cikin manyan alkawurran da gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi wa jama’ar akwai tabbatar da tsaro, alkinta tattalin arziki da janyo masu zuba jari sai kuma hada kai tare da tafiya da kowa ba tare da nuna banbancin bangaranci addini, kabila ko kuma siyasa ba.

Batun siyasa na ci gaba da dumama a jihar ta Kaduna, musamman la’akari da yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta fara zaman sauraren karar da jam’iyyar PDP ta shigar, tana Kalubalantar sakamakon zaben, wanda ta ce an yi aringizo, da kuma amfani da kudade wajen wannan zabe, baya ga tafka magudi.

Da bambancin kuri’u kasa da dubu 12 ne dai APC ta lashe zaben gwamna, abin da watakila ke ba PDP kwarin gwiwar samun nasara a kotu. 

To ko me ‚yan adawa a jihar zasu ce a game da wannan zaman shari’a da aka fara da kuma kamun ludayin gwamnatin da Uba Sani a Kaduna, Muhammad Dan Auta mai bai wa shugaban jam’iyyar PDP a jihar a Kaduna shawara ta fannin yada labarai, ya ce da alamu gwamnatin bata shigo da kafar dama ba, kasancewar ta shiga a cewarsa ta hanya mai cike da kazanta.

Da alama wadannan kalamai basu yiwa gwamnatin da magoya bayanta wani tasiri ba, don kuwa a cewar su basu da ko dar cewa sune zasu yi nasara a kotun,Muhammad Sani Akilu Idris shi ne mataimakin tsohon gwamna El-Rufa’I kan harkokin siyasa, yace akwai alamun haske idan aka lura da kamun ludayin gwamnan jihar cikin mako guda.

A yayin da jam’iyyu APC da PDP ke ci gaba da tabka zazzafar siyasa bisa kamun ludayin gwamnatin APC, mutanen jihar sun shaida wa DCL Hausa abubuwan da suka fata da kuma zullumi daga gwamnatin gwamna Uba Sani

Jihar Kaduna da ake yiwa kallo da cibiyar arewacin Nijeriya na da matukar tasiri wannan ta sa siyasarta ke daukar hankali, duk da dai jama’ar jihar na ganin akwai jan aiki gaban sabon shugaba Uba Sani.

 

DCL Hausa, Yacouba Umaru Maigizawa

Muna goyon bayan Tinubu da ya cire tallafin man fetur – CNG

 Muna goyon bayan Tinubu da ya cire tallafin man fetur inji kungiyar da ke kishin arewa 

Kungiyar nan da ke rajin ganin yankin arewacin Nijeriya ya cigaba da ake kira da CNG a takaice ta fito karara ta nuna goyon bayanta ga matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur.

Kungiyar mai hadakar kungiyoyi 150 ta caccaki tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, inda ta ce kudin da ake kashewa na tallafin man fetur Dala bilyan 15.6 a duk shekara ya isa a gina layin dogo daga Lagos zuwa Kano da kuma daga Port Harcourt zuwa Maiduguri da kuma Lagos zuwa Calabar.

Mai magana da yawun kungiyar Abdul’aziz Sulaiman a cikin takardar bayan taro da ya karanta a Kaduna, ya ce Naira tiriliyan 2.91 da gwamnatin Buhari ta kashe kan tallafin man fetur daga Janairu zuwa Disambar 2022, ne ya sa tattalin arzikin kasar ya durkushe.

Cinikin fetur ya ragu a gidajen man Nijeriya bayan cire tallafin man

Cinikin fetur ya ragu matuka a mafiyawancin gidajen man Nijeriya bayan cire tallafin man
Tashin gwauron zabin da farashin man fetur ya yi sanadiyyar cire tallafin man, ya sa gidajen mai babu ciniki sosai a ‘yan kwanakin nan a Nijeriya.
Wani bincike da Daily Trust ta gudanar, ya nuna cewa bayan farashin fetur din ya koma N537 a mafiyawan gidajen man, mutane sun fara kaurace wa, babu ciniki sosai.
Mafiyawan gidajen man, akwai man amma babu masu saye, har ma an gano cewa wasu mutane sun ajiye motocinsu ta dalilin tsadar fetur din.
Wani Manajan gidan mai a Kano, ya shaida cewa a baya, cikin kwanaki biyu suke sayar da fetur din su, amma yanzu yana iya cike mako cur ba a sayar ba.

Abba ya nada Dr. Baffa Bichi sakataren gwamnati da sauran wasu mukamai

 

Ga jerin mukaman da aka sanar kawo yanzu

1. Hon. Shehu Wada Sagagi, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati wato Chief of Staff.

2. Dr Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jiha.

3. Dr. Farouq Kurawa, babban sakatare na musamman wato PPS. 

4. Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, Chief Protocol

5. Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun gwamna.

Sanarwar da DCL Hausa ta samu daga Sunusi Bature Dawakin Tofa ta ce wadannan nade-nade sun fara aiki daga 29.05.2023 nan take.

Dikko Radda ya nada sakataren gwamnatin Katsina da wasu mukamai 10

Sabon Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Arch Ahmad Musa Dangiwa a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

A cikin wata sanarwa da Dikko Radda ya sanya wa hannu, ta ce Gwamnan ya kuma nada Jabiru Tsauri a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati. Kazalika, sanarwar ta ce, Gwamnan ya nada Barr Mukhtar Aliyu a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, sai Abdullahi Aliyu Turaji a matsayin PPS.

Sauran nade-naden su ne na Malam Maiwada Danmalam a matsayin Darakta Janar mai kula da kafafen yada labarai, Sai Ibrahim Kaula Mohammed a matsayin mai magana da yawun Gwamna da Abubakar Badaru Jikamshi a matsayin mataimaki na musamman ga Gwamna kan kafafen yada labarai.

Ganduje zai mika wa Abba mulkin Kano a Lahadi maimakon Litinin

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje zai mika wa sabon gwamna Abba Kabir Yusuf mulkin jihar Kano tun wannan Lahadi da misalin karfe 9pm a maimakon Litinin 29.05.2023 da aka tsara mika mulkin. 
Rahotannin da DCL HAUSA ta samu sun ce Ganduje zai yi haka ne domin ba shi damar halartar bikin rantsuwar kama aiki na Bola Ahmed Tinubu, wanda za a rantsar shi ma a Litinin din nan a matsayin shugaban Nijeriya na 16.
To amma duk da haka rahotanni sun ce zababben gwamnan Kanon zai yi bikin shan ruwarsa a Litinin kamar yadda aka tsara.

Na kyautata rayuwar talaka a mulkina – Buhari

                                                   Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa na shekaru takwas ya kyautata rayuwar talakawa a kasar. A jawabin bankwana da ya yi Nijeriya a ranar Lahadi ya ce mulkinsa ya taimaka wa mutanen da ke a yankunan karkara da sauran marasa karfi bunkasa rayuwarsu. 

Ya ce ya yi iyakar kokarinsa wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda ya ce ya kwato kudade masu yawa daga hannun barayin gwamnati domin kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya.

” Na gamsu cewa na dora Nijeriya a hanyar da ta dace, na kuma gamsu cewa zan bar Nijeriya fiye da yadda na tarar da ita a 2015” in ji Buhari

Ba zan ba ku kunya ba, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya

Zababben shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce ba zai ba ‘yan kasar kunya ganin yadda suka aminta suka zabe shi.

Bola Tinubu na magana ne bayan da shugaba Buhari ya lakaba masa kambin girmamawa na GCFR a fadar shugaban kasa, Abuja.
Ya ce ya san muhimmancin girmamawa da irin kalubalen da ke gabansa. Inda ya sha alwashin cewa ba zai ba ‘yan Nijeriya kunya ba.

Buhari ya ba da aikin inganta lantarkin Daura kan kudi Naira bilyan 4

Majalisar zartarwar tarayya ta amince da aiwatar da shirin ingantawa da samar da wutar lantarki a wasu sassan kasar nan.
Ministan lantarki na kasar Abubakar Aliyu bayan kammala taron majalisar zartarwar a ranar Laraba, ya ce ayyukan sun hada da sanya kayan aiki ma zamani a masarautar Daura jihar Katsina kan kudi Naira bilyan 4.

Abba Gida-gida ya bayyana kadarorinsa kafin fara aiki


Gabanin a yi bikin rantsar da shi a ranar Litinin, zababben gwamnan jihar Kano, Injiniya. Abba Kabir Yusuf ya bayyana ilahirin kaddarorin da ya mallaka da kuma bashin da ake bin shi a cikin wani kumshin takardu da ya mika a ranar Juma’a ga ofishin da’ar ma’aikata na jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma’a.
Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa zababben Gwamnan wanda ya samu tarba daga Daraktar a hukumar ta CCB ta jihar Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ya ce kwazonsa na bayyana kadarorin da ya yi nuni ne na gaskiya da rikon amana da zai zama ginshikin a gwamnati mai zuwa a jihar Kano.