DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a Katsina

-

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da kakkausar murya ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Kankara da Dutsinma a jihar Katsina.
Da yake bayyana wannan sabon harin da cewa abin takaici ne, shugaban kasar ya tabbatar da cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma karya lagon masu aikata ta’addanci a sassan kasar.
Shugaban kasar ya umurci jami’an tsaro da su yi dukkanin mai yiwuwa don bi ma wadanda aka halaka hakkinsu ta hanyar yin maganin wadanda suka yi wannan aika-aikar.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin jihar Katsina, iyalai da ‘yan’uwan wadanda harin ta’addancin ya rutsa da su, sannan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mr Ajuri Ngelale, wanda shi ne Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da DCL Hausa ta samu kwafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara