DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Zan iya rantsuwa da Alkur’ani ban saci dukiyar al’umma ba – ElRufa’i

-

 Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Naziru El-rufa’i ya ce ya shiga siyasa ne kawai don ya hidimta wa al’umma.

Google search engine

Tsohon Gwamnan ya kara da cewa ya tsunduma siyasa ne ba domin ya samu kudi ko satar dukiyar al’umma ba.

Malam El-rufa’i ya fadi haka ne a cikin wani shirin da Gidan rediyon Freedom Kaduna ya watsa da safiyar Talatar nan kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

A cikin shirin, Tsohon Gwamnan Malam Nasir El-rufa’i ya ce ya wadatu da abin da Allah Ya hore masa tun kafin ya zama Gwamna.

Malam El-Rufai ya ci gaba da cewa a shirye yake ya rantse da Al-Qur’ani a duk lokacin da tsofaffin gwamnonin jihae da na yanzu suka yi haka na tabbatar da cewa ba su taba karkatar da dukiyar al’umma ba.

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta tuhumi gwamnatin Naziru El-rufa’i da karkatar da sama da Naira biliyan 423 cikin shekaru takwas da ya yi yana mulki.

Tsohon gwamnan da na kusa da shi da aka tuhuma, sun musanta wadannan zarge-zargen, inda suka ce majalisar da gwamnatin jihar ne suke

farautar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan sandan jihar Katsina sun musanta labarin barayin daji sun karbe ikon karamar hukumar Kankara ta jihar

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce tana sane da wani labari da ta kira na karya da ake yadawa musamman a kafar sadarwar X...

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyarsa ta Al Nassr har zuwa shekarar 2027

Cristiano Ronaldo ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar Al Nassr ta kasar Saudiyya a hukumance, inda zai ci gaba da zama a birnin Riyardh na kasar...

Mafi Shahara