DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Asusun NELFUND ya ba daliban Nijeriya lamunin Naira bilyan 11

-

Asusun bayar da lamunin ilimi a Najeriya NELFUND ya sanar da cewa zuwa yanzu, ya raba rancen kimanin Naira biliyan 11 ga dalibai domin tallafa wa ilimi a kasar.
Shugaban hukumar, Akintunde Sawyerr ne ya bayyana haka yayin wata hira da Gidan Talabijin na Arise inda yake bayyana kudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin an sami sauki a harkar Ilmi
Sawyerr ya jaddada cewa ba za a bukaci wadanda suka ci gajiyar lamunin su biya bashin ba har sai bayan sun kammala bautar kasa da shekaru biyu ko kuma sun sami aikin yi. 
Sannan tsarin biyan lamunin a cewarsa, zai biyo ta hanyar zare wani kaso da bai taka kara ya karya ba daga albashin mai dauke da bashin a kowane wata cikin ƙayyadadden lokaci
Sawyerr ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne da nufin sassauta jin nauyi akan masu dauke da bashin da ba su riga sun sami aikin da zai biya musu bashin ba
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Shugaba Tinubu ta kirkiro shirin bayar da lamunin Ilmi ga É—aliban da suka cancanta, wanda zai ba su damar neman ilimi mafi girma ba tare da sun shiga matsalar neman kuÉ—i ba. 
Baya ga daliban Ilmi NELFUND ta sake jaddada aniyar ta ta tallafa wa fannin ilimin kirkira ga matasan Najeriya, da kuma samar masu da ayyukan yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

’Yan majalisar wakilai bakwai daga Akwa Ibom sun sauya sheka zuwa APC

Ana cigaba da samun rahotannin sauyin sheka a majalisar wakilai, yayin da ’yan majalisa bakwai daga Jihar Akwa Ibom suka koma jam’iyyar APC. Wadanda suka...

Jam’iyyar Labour tsagin Julius Abure ta ba Peter Obi sa’o’i 48 ya fice daga jam’iyyar saboda shiga hadakar ADC

Jam’iyyar Labour karkashin jagorancin Julius Abure ta bai wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, wa’adin sa’o’i 48 da ya fice daga jam’iyyar, bisa...

Mafi Shahara