DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya na ba kasashen Togo da Benin wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24, in ji kamfanin TCN

-

Manajan Daraktan 
kamfanin rarraba wutar lantarki a Nijeriya Sule Abdul’aziz ya sanar cewa kasar na ba kasashe makwabta na Togo da Benin wutar lantarki ta sa’o’i 24 a duk rana.
Sule Abdul’aziz ya sanar da hakan a lokacin da yake jawabi a wani shirin gidan talabijin na Channels.
 Ya kara cewa Nijeriya na samar da lantarkin ga wadannan kasashe kuma suna biya yadda ya kamata. 
Sai dai ya ce ko a Nijeriya ma akwai masu samun wutar lantarki ta sa’o’i 24, musamman waÉ—anda ke saman tsarin Band A, suna samun ta sa’o’i 20-22, kama yadda jaridar Punch ta rawaito.
Kamfanin TCN dai ya ce an tsara ba waÉ—anda suke saman tsarin Band A, wutar lantarki ta sa’o’i 20-24, sai na saman Band B aka tsara ba su wutar lantarki ta sa’o’i 16-20, sai waÉ—anda ke saman tsarin Band C aka tsara ba su wutar lantarki ta sa’o’i 16-20 a rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara