DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mabarata na nuna rashin jin dadinsu bisa yadda hukumomi a Abuja ke ci gaba da kama su

-

Masu Bara a Abuja

City & Crime ta rawaito cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya umarci jami’an gwamnatin da su tsafta ce babban birnin Abuja baki daya.Tun da farko dai ya baiwa mabarata zuwa ranar Lahadin da ta gabata da su fice daga titunan Abuja ko kuma a kama su.

Da suke mayar da martani a ranar laraba, wasu mabarata, masu bukata ta musamman, sun nuna rashin amincewarsu da matakin da aka dauka, inda suka bayyana damuwarsu a lokacin da suka ziyarci babban ofishin Daily Trust a Abuja.
Auwal I. Alhassan, wanda ya yi magana a madadinsu, ya soki mahukunta a birnin tarayya da rashin yin hulda da su, ko kuma magance korafe-korafensu kafin a ba da umarnin korar su.

Google search engine

Ya ce, abin takaici ne mahukuntan su ce sai sun koresu daga inda suke duk da suna da hakkin rayuwa a ko ina.

Ya kara da cewa, baya ga kungiyar SERAP, babu wata kungiya mai zaman kanta, ko kungiyoyin farar hula, ko kungiyoyin addini da suka kai musu dauki.

Alhassan ya yi ikirarin cewa wadanda aka kama suna rayuwa ne a cikin mawuyacin hali a gidan gyaran hali da ke Bwari, ba su da abinci, ruwa, da kuma kula da lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Lewandowski ba zai bar Barcelona a watan Junairu ba

Rahotanni na nuni da cewa Robert Lewandowski ba zai bar Barcelona a watan Janairu ba, amma akwai yiwuwar kashi 90 cikin 100 zai bar ƙungiyar...

Ka nemi yafiya bayan janye kalamanka na barazana ga Nijeriya – Barau Jibrin

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, ya caccaki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa barazanar kai wa Nijeriya hari da ya yi,saboda zargin ana...

Mafi Shahara