DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar sojin Nijeriya ta bai wa wata ‘yar jihar Borno tallafin karatu

-

Rundunar sojojin Nijeriya ta bai wa Nana-Fatima Bolori, wata hazika yar jihar Borno, tallafin karatu.

Google search engine

Kwamandan Rundunar Joint Task Force, Operation Hadin kai Manjo Janar Wahdi Shuaibu, da ke Arewa maso gabas ne ya sanar da haka a ranar Alhamis a Maimalari Cantonment da ke Maiduguri.

Manjo Shu’aibu ya bayyana cewa tallafin karatun na da nufin karfafa dangantakar sojoji da jama’a da kuma samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar da ya dace.

A cewarsa, tallafin da za a bata zai biya kudin karatun ta wanda zai tallafa mata har ta samu nasarar a rayuwar ta,saboda tallafi a harkar ilimi yana da matukar muhimmanci

Ya kara da cewa wannan yunƙurin ya yi daidai da ra’ayin babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja na tallafa wa marayun da suka yi abin yaba wa da kuma ƙwazo a manyan makarantun gwamnati na Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaban Amurka Donald Trumph ya haramtawa Farfesa Wole Soyinka zuwa kasar

Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaba Donald Trump ta soke takardar izinin shiga ƙasar ga Farfesa Wole Soyinka, sanannen marubuci a duniya. Farfesa Soyinka ya bayyana hakan...

Hukumar agajin gaggawa NEMA ta karɓi ƴan Nijeriya 153 da suka makale a Chadi

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA, ta bayyana cewa ta karɓi ’yan Nijeriya 153 da suka dawo daga ƙasar Chadi, ƙarƙashin shirin Ƙungiyar...

Mafi Shahara