DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ta musanta fashewar wani abu mai hatsari a Kasuwar Terminus dake yankin Jos ta arewa.

-

Mai magana da yawun rundunar, Alfred Alabo wanda ya sanar da hakan a cikin wani bayani da ya fitar, ya ce sun sa mu rahoton cewa, an dasa wani abin fashewa a cikin rame a yankin, abin da ya razana al’umma. 
Alabo ya ce ba su yi hanzari ba Kwamishinan yan sanda na jihar ya tura jami’an da ke kwance bam domin bincike, kuma babu wani abin fashewa da suka gano a wurin. 
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wata fashewa mai karfi ta faru a birnin Jos na jihar Plateau da safiyar yau Talata, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai a jihar Kebbi da DCL Hausa ta yi rahoton zargin da ake yi masa...

Lantarkin N40.61bn ta salwanta tun kafin ta kai ga masu amfani a Nijeriya – NERC

Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya(NERC) ta bayyana cewa an yi asarar wutar lantarki da ta kai Naira biliyan 40.61 a layukan ba da lantarki,...

Mafi Shahara