DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sarakuna ba sa tsoron gwamnoni, mutunta kansu kawai suke yi – Sarkin Musulmi

-

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya musanta ikirarin cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin jihohi a Nijeriya, yana mai cewa sarakunan gargajiya ne ke mulkin kasar tun kafin yanzu, inda ya ce a matsayinsu na sarakuna sun fi gwamnoni fahimtar kasar.
Sarkin Musulin ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki kan ci -aban matasan Arewacin Najeriya da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ta shirya a Abuja ranar Talata.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce sarakuna na mutunta kawunansu ne ta hanyar kauce wa tsoma baki kan al’amurra, yana shugabannin na gargajiya na mutunta ikon da gwamnoni ke da shi a jihohin. Ya ce bai kamata a dauki hakan a matsayin tsoro ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon kwamishinan Ganduje ya soki gwamnatin Abba bisa zargin sayar da filin makarantar

Tsohon kwamishinan ilimi na a zamanin Ganduje, Muhammad Sanusi Sa'id Kiru, ya soki matakin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na mayar da Makarantar Sakandare ta ‘Yan...

Hukumar zabe za ta hada kai da majalisar wakilan Nijeriya domin gudanar da sahihin zabe

Shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da Majalisar Dokoki domin tabbatar da gudanar da sahihin...

Mafi Shahara