DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya rushe majalisar gudanarwa ta jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke jihar Anambra

-

Shugaba Tinubu

A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar ya ce rushe majalisar gudanarwar ya biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa akwai wasu abubuwa da majalisar ke yi ba bisa ka’ida ba.

Google search engine

Gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda majalisar ta nuna rashin kula da dokokin jami’ar wajen zaben wasu shugabanni.

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya kuma rushe shugabancin Engr. Ohieku Muhammed Salami a matsayin Pro-chancellor kuma shugaban majalisar gudanarwa na jami’ar tarayya ta kimiyar lafiya dake Otukpo a jihar Benue.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara