DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tabbas akwai yunwa a Nijeriya amma sauki na zuwa – Shugaba Tinubu

-

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta mayarda hankali wajen saka jari a bangaren noma da kiwo domin magance rikicin manoma da makiyaya da kuma bunkasa tattalin arziki.
Shugaban wanda ke jawabi a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, ya kuma jaddada cewa akwai matsalar yunwa a kasar, sai dai gwamnatin sa na kokarin ganin abubuwa sun daidaita.
Tinubu ya fadi haka ne a yayin da yake sanya hannu ga wata yarjejeniyar saka hannun jarin dala biliyan 2.5 da kamfanin JBS S.A, daya daga cikin manyan kamfunnan da ke sarrafa nama a fadin duniya.
Ya ce wannan yarjejeniya za ta magance matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya da ta jima tana damun al’umma a wannan nahiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ƴan Nijeriya sun gargadi Turai kan barazanar da Wike ke yi wa demokradiyya a ƙasar

Kungiyar Nigeria Unite ta kai karar minista Nyesom Wike zuwa ga Kungiyar Tarayyar Turai Ministan Abuja Nyesom Wike ya dauko hanyar kassara dimukuradiyya a Nijeriya....

Libya ta kora ‘yan Nijeriya 80 gida saboda zama ba bisa ka’ida ba a kasar

Hukumomin Libiya sun kori ’yan Nijeriya 80 daga ƙasar bayan kama su suna zama ba bisa ƙa’ida ba, a wani yunkuri na rage cinkoso a...

Mafi Shahara