DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya na bin diddigin shafukan sada zumunta na ‘yan bindiga

-

Gwamnatin tarayya ta ce tana sane da yadda shafukan ‘yan ta’adda ke kara bazuwa a kafafen sada zumunta na zamani a cikin ‘yan kwanakinnan.
Wannan na zuwa ne yayin da ayyukan ‘yan bindiga ke kara karfi a shafukan sada zumunta musamman Tiktok, inda su ke nuna bindiogogi da kuma kudade zube birjik tare da yin barazanar cewa sun fi karfin gwamnati.
A wata hira da jaridar Punch, kodinetan cibiyar yaki Da ta’addanci da ke karkashin ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj. Gen. Adamu Laka, ya ce gwamnati na aiki tukuru domin ganin ta yaki ‘yan ta’addan ta wannan hanyar da suka ɓullo da ita.
Kodinetan ya kira ‘yan bindigar matsorata inda kalubalance su da su fito a yi gaba da gaba da jami’an tsaro ba wai labewa suna barazana ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara