DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a kammala gyaran matatar man Kaduna zuwa karshen Disamba 2024

-

Manajan daraktan matatar mai ta Kaduna Dr. Mustafa Sugungun ya ce ana sa ran kammala gyaran da ake yiwa matatar Kaduna zuwa karshen shekararnan ta 2024.

Google search engine

Kamfanin mai na kasa NNPCL ne ya bayar da kwangilar gyaran wani bangare na na matatar mai ta Kaduna ga kamfanin kasar Koriya ta Kudu ‘Daewoo Engineering & Construction’ akan kuɗi dala miliyan 741.

Bayan kammala gyaran, matatar wadda ke aka gina domin tace ganga 110,000, za ta rika tace kashi sittin na gangar mai 66,00 a kowace rana.

A jawabinsa, babban manajan wanda ya samu wakilcin manajan sashen ayyuka na matatar Mista Emmanuel Ajiboye, a wurin kaddamar da aikin gyaran wata makaranta da kamfanin ya yi, ya ce idan aka kammala gyaran matatar za ta samar da ayyukan yi, bunƙasa kasuwanci da kananan sana’o’i a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Atiku martani cewa babu yunwa a Niijeriya

Fadar shugaban kasa ta ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tafiya kan madaidaiciyar hanya, tana mai musanta ikirarin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da...

Kotu ta daure wani dan Nijeriya a Amurka kan laifin zambar kudin gado

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Ehis Lawrence Akhimie hukuncin daurin shekaru fiye da takwas bayan an same shi...

Mafi Shahara