DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin matatar Fatakwal ya fi tsada akan na matatar Dangote da naira 75

-

Kungiyar masu sarin mai ta Najeriya PETROAN, ta ce farashin fetur a matatar Fatakwal da ta soma aiki a wannan Talata ya fi na matatar Dangote tsada da naira 75.
Jami’in yada labarai na kungiyar Dr. Joseph Obele ne ya bayyana haka a lokacin bude matatar wadda za ta rika tace ganga 60,000 a kowace rana, inda ya ce farashin matatar Dangote naira 970 ne, yayinda a matatar gwamnati ke sayarwa a 1,045.
Dr Obele, ya bayyana damuwa akan yadda banbancin farashi zai iya kawo matsala ga kokarin da ake yi na daidaita farashin man fetur a fadin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin kasar na kan hanyar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 cikin shekaru goma masu zuwa. Kashim...

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da direba da fasinjoji a Katsina

Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau a Katsina. Jami’an sun yi artabu da ‘yan...

Mafi Shahara