DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta bada umarnin ci gaba da tsare Yahaya Bello har sai 10 ga watan Disamba

-

Mai shari’a Maryanne Anenih ta kotun babban birnin tarayya Abuja, ta bada umurnini ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a hannun hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Alkaliyar kuma ta dage shari’ar har sai 10 ga watan Disamba 2024 domin yanke hukuncin akan bukatar bayar da shi beli.
An gurfanar da Yahaya Bello ne tare da wasu mutane biyu; Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu, akan zarge-zarge 16 wadanda suka musanta aikatawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawa ta bukaci a dauki matasa aikin tsaro domin magance matsalar tsaro

Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla...

Matukar dimokradiyya ta gaza a Nijeriya sai ya shafi fadin Yammacin Afrika – ECOWAS

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a...

Mafi Shahara