DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta rufe wata coci a Lagos bisa zargin damfara

-

Wata babbar kotun jihar Lagos da ke zaune a Ikeja, ta yanke wa wasu ma’aurata, Harry Uyanwanne da Oluwakemi Odemuyiwa, hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari tare kuma soke rijitar majami’ar Temple International. 

Mai shari’a Mojisola Dada ta yanke hukuncin ne bayan ta same su da laifukan da ake tuhumarsu.
Tun da farko dai hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a gaban kotu, inda take tuhumarsu, da amfani da majami’ar wajen damfarar mutane, tare da yi musu zambo cikin aminci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai zama a San Gabriel Valley, Abiola Femi Quadri, hukuncin ɗaurin shekara 11 da wata...

Natasha ta sake shan alwashin komawa majalisar dattawa a ranar Talata

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar Majalisar Dattawa daga jihar Kogi da aka dakatar, ta shigar da ƙara ga Majalisar Dattawa tana neman su girmama hukuncin Babbar...

Mafi Shahara