DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya da makwabtan kasashe sun soma fatattakar Lakurawa

-

Nijeriya da Nijar, da kuma Chadi da wasu makwabtan kasashe sun yi haɗaka wajen fatattakar ‘yan kungiyar Lakurawa da suka addabi iyakokin kasar.
Wannan hadakar na da manufar kakkabe ‘yan ta’addan da ke aiwatar da miyagun ayyuka a kasashen Nijeriya da kasashen dake kewaye da ita.
 
Da yake karin haske akan matakan da suke dauka, daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron Nijeriya Manjo-Janar Edward Buba, ya shaidawa jaridar Punch cewa hadin gwuiwar kasashen wajen sintiri akan iyaka zai rufe duk wata mafaka da Lakurawa za su bi domin shiga kasashen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Barnar da jam’iyyar APC ta yi wa Nijeriya ta zarta ta mulkin soja – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC mai mulki da lalata tsari da yanayin kasar, yana mai bayyana ta a matsayin jam'iyya...

Al’umma ne ke taka rawa wajen nasara a zabe ba gwamnoni ba – Aregbesola ga APC

Sakataren jam'iyyar ADC a Nijeriya ya gargadi APC mai mulki cewa al'umma ne ke taka rawa wajen nasara a zabe ba gwamnoni ba. Ra'uf Aregbesola ya...

Mafi Shahara