DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Facebook, Instagram da WhatsApp sun samu tangardar na’ura

-

Facebook, Instagram da WhatsApp sun samu tangardar na’ura

Miliyoyin masu amfani, manyan mahajojin kamfanin Meta da suka hada da Facebook da Instagram, da kuma WhatsApp, a fadin duniya na fuskantar tutsu.

Rahotannin da suka mamaye shafukan sada zumunta, ciki har da X, sun tabbatar da cewa lamarin ya zama kamar wutar daji, inda miliyoyin masu amfani suka kasa shiga shafukansu.

Google search engine

Wani dandali da ke bin diddigin abubuwan da suka faru, ya nuna yadda aka rinka tura rahotannin samun tangardar shafukan. 

Rahotanni sun nuna cewa masu amfani da Instagram sama da dubu 71 sun shigar da korafi game da tangardar,  yayin da masu amfani da Facebook suka aika korafe-korafe sama da dubu 107 daga sassan duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

’Yan sanda sun kama mutanen da ake zargi da satar kifi a jihar Neja

Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta sanar da kama mutane hudu bisa zargin sata da kuma karɓar kayan sata, bayan da aka sace kifaye da...

Manoma a Nijeriya sun koka kan shirin karya farashin kayan abinci

Manoma da masu sarrafa shinkafa a Najeriya sun soki manufofin gwamnatin tarayya bayan da alkaluma suka nuna cewa yawan kudaden shigo da kayayyakin gona ya...

Mafi Shahara