DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ko da Atiku da Obi sun yi maja ba za su iya kayar da Tinubu ba – Jam’iyyar APC

-

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ce ba wata haɗaka da ‘yan adawa Atiku Abubakar tsohon shugaban kasa da Peter Obi tsohon gwamnan Anambra za su yi, da za ta iya zama barazana ga sake zaben Shugaba Tinubu a shekara ta 2027.
Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC na kasa Bala Ibrahim ne ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar Punch.
Bala Ibrahim na mayar da martani kan kalaman mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe cewa, mai gidansa Atiku da Obi sun dauki darasin abinda ya faru a zaɓen da ya gabata kuma za su hada kai domin kawar da gwamnatin APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kama Maduro da Amurka ta yi

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro. Ramaphosa ya...

Sojoji sun ceto mutane shida da aka sace a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarar ceto mutane shida da aka sace a wani sumame da suka gudanar a yankunan Kajuru da Kujama...

Mafi Shahara