Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ce ba wata haɗaka da ‘yan adawa Atiku Abubakar tsohon shugaban kasa da Peter Obi tsohon gwamnan Anambra za su yi, da za ta iya zama barazana ga sake zaben Shugaba Tinubu a shekara ta 2027.
Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC na kasa Bala Ibrahim ne ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar Punch.
Bala Ibrahim na mayar da martani kan kalaman mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe cewa, mai gidansa Atiku da Obi sun dauki darasin abinda ya faru a zaɓen da ya gabata kuma za su hada kai domin kawar da gwamnatin APC.