DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Vinicius Jr ya zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya

-

Dan wasa Vinicius Jr

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta kaarrama dan wasan  gefe na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da tawagar Brazil Vinicius Jr a matsayin gwarzon dan  wasa na shekara ta 2024.

Dan wasan mai shekaru 24 a baya dai yana cikin jerin yan wasan da suka yi takarar gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya wato Ballon d’Or, wanda dan wasa Rodri na Manchester City ya lashe.

Google search engine

Vinicius dai ya taimaka wa kungiyarsa ta Madrid wajen lashe gasar zakarun Nahiyar Turai da ta La Liga na kakar shekerar 2023-24, inda ya ci kwallaye 24 tare da taimakawa a zura kwallo har sau 11.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kenya da Senegal sun kulla yarjejeniyar shige da fice ba tare da biza ba

Gwamnatocin Kenya da Senegal sun bai wa juna damar shige da fice ga 'yan kasashensu ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 90. DW Africa...

Majalisar dattawan Nijeriya ta bukaci gwamnati ta kara wa sojoji albashi

Majalisar dattawan Nijeriya ta bukaci gwamnati ta sake yin duba kan albashin da ake biyan jami'an tsaro musamman ma soji a fadin kasar. Majalisar ta bayyana...

Mafi Shahara