DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane biyu da ake zargi da satar Keke-napep

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar Keke-napep tare da hannunta ababen hawan da ta gano ga masu su.
A cewar wani bayani da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna ya fitar, rundunar ta samu wannan nasara ne bayan wani samame da ta kai a maboyar bata garin da ke karamar hukumar Dambatta a ranar 9 ga watan Disamban da muke ciki.
A yayin samamen an kama wani Ado Yusuf, mai shekaru 40 da kuma Rabi’u Suleiman, mai shekaru 35, tare da kwato Keke-napep biyu da aka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan majalisar wakilan Nijeriya ya sauys sheka daga PDP zuwa ADC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC. A cikin wasiƙar...

Sanata Wamako ya raba wa marayu su 10,000 tallafin N1,000 kowane a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da tallafin miliyan 10, ga mutane dubu 10 da...

Mafi Shahara