Wata Kotu ta sake bayarda belin Yahaya Bello kan miliyan 500

-

Mai shari’a Maryanne Anenih ta kotun babban birnin tarayya Abuja ta bada tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello akan tsabar kudi N500 da kuma gabatar da mutum uku da za su tsaya masa.
Wannan na zuwa ne bayan da a makon da ya wuce wata kotun, karkashin jagorancin Mai shari’a Emeka Nwite ta bayarda belin Yahaya Bello a kan wadannan sharuddan.
Tsohon gwamnan na fuskantar tuhume-tuhume a kotunan biyu kan zargin badakalar kudade biliyan 110 da kuma wasu biliyan 80.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara