DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rahoton IMF na 2024 ya cire Nijeriya daga ƙasashe 10 da suka fi tarin bashi

-

Sabon rahoton jami’an Hukumar Bayar Da Lamuni Ta Duniya (IMF) ya nuna ƙasashen Afrika da aka fi bi bashi a shekara ta 2024 inda ya bayyana ƙasar Misira a matsayin wacca take da bashi mafi girma a Afrika da ya zarce Dalar Amurka Biliyan 9. 
Rahoton ya nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Jun na wannan shekarar ta 2024, gwamnatin Najeriya ta biya sama da Dalar Amurka Biliyan 2.24 na basukan da ake bin ƙasar wandanya fitar da ita daga ƙasashen da bashin yayi musu ƙatutu. 
Rahoton da ofisin kula da basussuka na Najeriya ya fitar ya nuna cewa a watanni 3 na farkon shekarar nan ta 2024, gwamnatin Najeriya ta biya Dalar Amurka Biliyan 1.12 na bashin da ake bin ta. A watanni 6 na shekarar ta dake biyan Dalar Amurka Biliyan 1.12 ga ƙasashe fa kuma hukumomin da ke bin ta bashi da suka haɗa da IMF da Babban Bankin Duniya. 
Wannan cigaban ya samu ne sakamakon matakin da gwamnatin Tinubu ta ɗauka na dena almubazzaranci da kuɗaɗen ƴan ƙasa musamman cire tallafin Man Fetur wanda ya taimaka wajen samun ƙarin kudade ga Jihohi da ma ƙasar baki ɗaya don ayyukan raya ƙasa da al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu ya yi kira da a zauna lafiya gabanin zaɓen Abuja, Kano da Rivers

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a, jami’an tsaro da jami’an Hukumar zaɓe Mai zaman kanta (INEC) da su gudanar...

Gwamnatin Nijeriya za ta kafa kwalejin koyon likitanci ta sojoji don magance karancin likitoci

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin kafa kwalejin koyon likitanci ta soji "Armed Forces College of Medicine and Health Sciences" a matsayin wani mataki na...

Mafi Shahara