DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta rage kasafin kudin 2025 zuwa Naira Biliyan 384

-

Majalisar dokokin Nasarawa ta rage kasafin kudin 2025

Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta zaftare kasafin kudin shekarar 2025 da aka amince da shi a baya daga Naira biliyan 402 da miliyan 500 zuwa Naira biliyan 384 miliyan 300. 

Kakakin majalisar, Danladi Jatau, shi ne ya sanar kwaskwarima a kasafin kudin, a wani zaman gaggawa da majalisar ta yi ranar Juma’a a garin Lafiya babban birnin jihar.

Jatau, ya kuma ce rage kasafin ya biyo bayan shawarar da majalisar zartarwar jihar ta bayar, cewa kasafin kudin da aka yi a baya ya haura kudaden shigar da jihar ke samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwamishinan Jigawa ya mayar da rarar Naira miliyan 301 daga kudaden da aka ware don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya mayar da Naira miliyan 301 zuwa baitul malin jihar, daga cikin Naira biliyan...

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta karɓi wasikun kulla kawance daga sabbin jakadun ƙasashe 8

A ranar Juma’a, 9 ga Mayu, 2025, fadar gwamatin ta Jamhuriyar Nijar ta karɓi sabbin jakadun daga jakadun ƙasashen duniya guda takwas. Inda shugaban mulkin sojin...

Mafi Shahara