DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Wata fashewa ce da ta biyo baya ta kashe mutane a Sokoto ba harin jirgin sama ba – Hedkwatar tsaron Nijeriya

-

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta alakanta mutuwar mutane 10 a jihar Sokoto bayan wani harin jirgin sojin sama da wata fashewa da ta biyo baya.
Kwana biyu da suka wuce, gwamnatin jihar Sokoto ta ce mutum 10 sun mutu yayinda wasu da dama su ka jikkata a wasu kauyukka a karamar hukumar Silame bayan harin da jirgin saman sojoji ya kai wa mutanen bisa kuskure.
Sai dai a sanarwar da ya fitar, daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro Manjo Janar Edward Buba, ya ce mace mace da jikkatar da aka samu ba saboda farmakin soji ne kai tsaye ba, wata fashewa ce da ta biyo baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Nijeriya ta musanta zargin leken asiri kan jirginta da ke Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta musanta zargin leken asiri da ake jinginawa jirginta a Burkina-Faso Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da...

Dangote ya zayyana irin zagon kasan da ake yi wa matatun mai a Nijeriya

Shugaban matatar man Dangote, Aliko Dangote, ya ce kungiyoyin da ke zagon kasa a bangaren mai da gas a Najeriya da ya kira “oil mafia”...

Mafi Shahara