DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin jihar Zamfara ta nemi agajin tarayya, bayan Bello Turji ya yi barazanar kaddamar da hare-hare a wasu yankunan jihar

-

Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki kan kasurgumin dan bindiga Bello Turji, bayan da ya yi barazanar kai hare-hare kan al’ummomin Zamfara da Sokoto.
A cikin wani bidiyo da ya fitar a ranar Laraba, Turji ya ce idan har jami’an tsaro ba su saki makusancinsa Bello Wurgi da aka kama ba to zai hana zaman lafiya a yankin.
Da yake mayarda martani kan barazanar, mai baiwa gwamnan jihar Zamfara shawara kan hulda tsakanin hukumomin gwamnati Dr Sani Shinkafi ya yi kira ga Shugaban Bola Ahmad Tinubu da ya dauki matakin gaggawa kan wannan batu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050,...

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba...

Mafi Shahara