![]() |
Shugaba Tinubu |
Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi kira da gwamnatocin jihohi da su hada gwiwa domin tunkarar kalubalen da ke addabar kananan hukumomi a kasar.
Shugaba Tinubu ya yi wannan kiran ne a yayin bikin sabuwar shekara tare da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da wasu gwamnonin Nijeriya da suka yi a gidansa da ke Legas ranar Laraba.
Da yake bayyana kudirinsa na ci gaban kananan hukumomi, a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya jaddada muhimmancin ‘yan cin gashin kai ga kananan hukumomi wajen ci gaban kasa da tare da kawar da rade radin rashin jituwa tsakanin sa da gwamnonin.
Inda ya ce babu wata matsala a tsakanin su,illa kokarin kawo sauyi mai dorewa ga kasa ta hanyar baiwa kananan hukumomi dama.