DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ana zargin wata amarya da saka guba cikin abincin buki har ya yi ajalin mutum guda tare da kwantar da ango a Asibiti

-

 

Amarya da Ango

Google search engine

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Jahun da ke jihar Jigawa.

Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa jaridar PUNCH cewa,ana zargin wani dan kasuwa ne ya sa amaryar ta aikata hakan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce ana ci gaba gudanar da bincike akai.

A cewar sa ‘yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin sanya guba a cikin abincin, wadanda ake zargin su biyun amaryar ce da wata mace, ya kara da cewa suna tsare kuma ana yi musu tambayoyi daga sashin binciken manyan laifuka na rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan majalisar wakilan Nijeriya ya sauys sheka daga PDP zuwa ADC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC. A cikin wasiƙar...

Sanata Wamako ya raba wa marayu su 10,000 tallafin N1,000 kowane a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da tallafin miliyan 10, ga mutane dubu 10 da...

Mafi Shahara