DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dan wasan Najeriya Sadiq Umar ya kammala komawa kungiyar Valencia

-

Dan wasan gaba na tawagar kwallon kafa ta Real Sociedad dake buga gasar La liga ta kasar Spain , Sadiq Umar ya kammala komawa tawagar Valencia CF dake kasar ta Spain a matsayin aro na wata shida.
Mai shekaru 26, dan wasan dan asalin jihar Kaduna kuma dan wasan gaba na tawagar Najeriya wato Super Eagles, ya koma ne bayan cimma yarjeniya da Valencia, a yayin da aka bude kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu.
Sadiq zai yi amfani da riga mai lamba 12 a tawagar ta Valencia, abinda hakan ke zama wani sabon shafi ga dan wasan da yayi fama da jinyar raunin da ya samu a kakar shekarar bara ta 2023/24, wanda ya hana shi buga gasar kofin Afirka na AFCON, da Najeriya ta zo a mataki na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Daga 2026 ₦500,000 kawai ɗan Nijeriya zai iya cira a banki cikin sati ɗaya – CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake fasalin dokokin cire kuɗi daga bankuna kan sabon tsarin da zai fara aiki daga watan Janairun 2026. Babban bankin ya...

Ƴan kwangila sun girke akwatin gawa a ofishin ma’aikatar kuɗin Nijeriya

‘Yan kwangila sun girke akwatin gawa a kofar shiga ofishin ma’aikatar kudin Nijeriya da ke Abuja.   ‘Yan kwangilar, karkashin inuwar kungiyarsu ta 'yan asalin Nijeriya sun...

Mafi Shahara