DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaban karamar hukuma a Kaduna ya ƙara wa Limamai alawus

-

Shugaban karamar hukumar Soba a jihar Kaduna Muhammad Lawal Shehu, ya bayar da umurnin kara kudin alawus da ake bai wa limaman masallacin juma’a da ke yankin.
Da yake jawabi ga limaman, Honarabul Lawal ya bayyana cewa bayan rantsar da shi ya lura da cewa abin da ake bai wa malamai ba yawa kuma ana shafe tsawon lokaci ba a biya su alawus ba.
Shugaban karamar hukumar ya ce wannan ne yasa ya bayar da umurnin sanya karin wasu limamai cikin tsarin biyan alawus din tare da kara yawan kuɗaɗen da ake biyansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara